ABNA24 : Kafin haka dai kamfanin ya rufe shafukkan Twitter da dama na ma’aikatan kamfani a ranar 26 ga watan Octoban da ya gabata, don takurawa kasar ta amince da bukatun Amurka. Sai dai kamfanin ya bada labarin cewa takunkuman tattalin arzikin da Amurka ta dorawa kanfanonin man fetur a kasar basu hanasu saiya man fetur da suke samarwa ga masu sayansu a kasashen waje ba. Wasu rahotannin sun bayyana cewa a halin yanzu Iran tana sayarda ganga miliyon 1.5 a ko wace rana. A shekara ta 2018 ne gwamnatin Trump ta fice daga yarjejeniyar JCPOA ta shirin nukliyar kasar Iran sannan ta dora mata takunkuman tattalin arziki wadanda zasu hana kasar saida danyen man da ta dogara da shi wajen sarrafa tattalin arzikin kasar.
342/